Tsallake zuwa abun ciki
Ezekiyel 18:1-4

Karyata karin maganar laifin gādo

Ezekiyel 18:1-4
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa, “ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?
3
“Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.
4
Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options