Ezekiyel 14:1-8
1
Waɗansu dattawan Isra’ila suka zo wurina suka zauna a ƙasa a gabana.
2
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
3
“Ɗan mutum, waɗannan mutane sun kafa gumaka a cikin zukatansu suka sa mugayen abubuwan sa tuntuɓe a gabansu. Zan bar su, su taɓa nemi ni?
4
Saboda haka ka yi musu magana ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da wani mutumin Isra’ila ya kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuma sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina game da babban bautar gumakarsa.
5
Zan yi haka don in sāke ƙame zukatan mutanen Isra’ila, waɗanda duk suka yashe ni don gumakansu.’
6
“Saboda haka ka faɗa wa gidan Isra’ila cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tuba! Ku juyo daga gumakanku ku kuma furta dukan ayyukanku masu banƙyama!
7
“ ‘Duk sa’ad da mutumin Isra’ila ko baƙo mai zama a Isra’ila ya rabu da ni ya kuma kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuna sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi don yă neme ni, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina.
8
Zan yi gāba da mutumin in kuma sa ya zama misali da kuma abin karin magana. Zan ware shi daga mutanena. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
Settings