Skip to content
Fitowa 37:10-12

Fitowa 37:10-12

10
Suka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa ƙafa ɗaya, tsayinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi.
11
Sa’an nan suka dalaye shi da zinariya zalla, suka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.
12
Suka kuma yi masa baki mai fāɗin tafi hannu, suka yi zubin zinariya a bisa bakin.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options