Skip to content
Fitowa 36:31-34

Fitowa 36:31-34

31
Suka kuma yi sanduna na itace ƙirya, biyar domin katakan da suke a gefe guda na tabanakul,
32
biyar domin waɗanda suke ɗayan gefen da kuma biyar domin katakan da suke gefen yamma na iyaka ta ƙarshen tabanakul.
33
Suka sa sandan da yake a tsakiya yă wuce daga wannan gefe zuwa wancan.
34
Sai suka dalaye katakan da zinariya, suka yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Suka kuma dalaye sandunan da zinariya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options