Fitowa 20:8-12
8
Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki.
9
Kwana shida za ka yi dukan aikinka,
10
amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.
11
Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
12
Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
Settings