Dokoki shida na ƙarshe: Aikin mutum ga maƙwabcinsa
12
Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
13
Ba za ka yi kisankai ba.
14
Ba za ka yi zina ba.
15
Ba za ka yi sata ba.
16
Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.
17
Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”
Settings