Skip to content
Fitowa 16:22-26

Fitowa 16:22-26

22
A rana ta shida, suka tattara ninki biyu, mudu biyu ga mutum guda, sai shugabannin taron suka zo suka kawo ƙara wurin Musa.
23
Shi kuma ya ce musu, “Wannan shi ne umarnin Ubangiji, ‘Gobe za tă zama ranar hutu, Asabbaci mai tsarki ga Ubangiji. Domin haka sai ku toya abin da kuke so ku toya, ku kuma dafa abin da kuke so ku dafa. Abin da ya rage ku ajiye har safe.’ ”
24
Sai suka bar saura har safe, kamar yadda Musa ya umarta, bai kuwa yi wari ko yă yi tsutsa ba.
25
Musa ya ce, “Ku ci shi yau, saboda yau Asabbaci ne na Ubangiji. Ba za ku same shi a ƙasa a yau ba.
26
Kwana shida za ku tattara shi, amma a rana ta bakwai, Asabbaci, ba za a same shi ba.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options