Skip to content
Fitowa 16:13

Fitowa 16:13

Ana nuna aya 13 tare da mahallin da ke kewaye.
10
Yayinda Haruna yake magana da dukan taron Isra’ila, sai suka duba wajen hamada, sai ga ɗaukakar Ubangiji tana bayyana a girgije.
11
Ubangiji ya ce wa Musa,
12
“Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, ‘A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”
13
Da yamman wannan rana, sai makware suka rufe dukan sansani, da safe kuma sai ga raɓa ta kewaye sansani.
14
Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa.
15
Sa’ad da Isra’ilawa suka ga wannan, sai suka ce wa junansu, “Mene ne wannan?” Gama ba su san ko mene ne ba. Musa ya ce musu, “Wannan shi ne burodin da Ubangiji ya ba ku ku ci.
16
Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Kowane mutum zai tattara bisa ga bukatarsa. Ku tara rabin gallon don mutum guda da yake cikin tentinku.’ ”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 90 chars

Options