Fitowa 14:21-28
21
Da Musa ya miƙa hannunsa a bisa teku, sai Ubangiji ya tura teku baya da iskar gabas mai ƙarfi duk dare, ya maishe shi busasshiyar ƙasa. Ruwa ya rabu,
22
sai Isra’ilawa suka wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa, ruwan ya zama musu katanga dama da hagu.
23
Masarawa suka bi su da dukan dawakan Fir’auna, da kekunan yaƙi, da mahayan, suka bi su cikin teku.
24
Da asubahin fāri, sai Ubangiji ya dubi ƙasa a kan sojojin Masarawa daga al’amudin wuta da kuma girgije, sai ya sa suka ruɗe.
25
Ya sa ƙafafun keken yaƙinsu suka fita don su kāsa tuƙi. Sai Masarawa suka ce, “Bari mu gudu daga Isra’ilawa gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masar.”
26
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa teku don ruwa yă koma kan Masarawa, da keken yaƙinsu, da kuma mahayansu.”
27
Musa ya miƙa hannunsa a bisa tekun, da wayewar gari kuwa teku ya koma wurinsa na dā. Masarawa suka yi ƙoƙari su gudu, sai Ubangiji ya tura su cikin teku.
28
Ruwan ya komo ya rufe keken yaƙin da mahayan, dukan sojojin Fir’aunan da suka bi bayan Isra’ilawa cikin teku, ba ko ɗaya da ya tsira.
Settings