Fitowa 1:15-21
15
Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce,
16
“Sa’ad da kuke taimakon matan Ibraniyawa lokacin haihuwa, in jaririn namiji ne ku kashe shi, amma in ta mace ce, ku bar ta da rai.”
17
Amma ungozomomin nan masu tsoron Allah ne, ba su kuwa aikata abin da sarkin Masar ya gaya musu ba; suka bar jarirai maza su rayu.
18
Sai sarkin Masar ya kira ungozomomin, ya tambaye su ya ce, “Don me kuka yi haka? Don me kuka bar jarirai maza su rayu?”
19
Ungozoman suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Ai, matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gwarzaye ne, sukan haihu kafin ungozomomin su kai wurinsu.”
20
Saboda haka Allah ya nuna alheri wa ungozomomin, Isra’ilawa kuwa suka yi yawa fiye da dā.
21
Saboda ungozomomin suna tsoron Allah, sai Allah ya ba su iyalan kansu.
Settings