Esta 9:31-32
31
don a kafa waɗannan ranakun Furim a keɓaɓɓen lokacinsu, kamar yadda Mordekai mutumin Yahuda da Sarauniya Esta suka dokace su. Yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu, game da lokutansu na azumi da makoki.
32
Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan umarnai game da Furim, aka kuma rubuta ta cikin tarihi.
Settings