Skip to content
Esta 9:29-32

Esta 9:29-32

29
Saboda haka Sarauniya Esta, ’yar Abihayil, tare da Mordekai mutumin Yahuda, suka rubuta da cikakken iko, suka tabbatar da wannan wasiƙa ta biyu game da Furim.
30
Mordekai kuwa ya aika da wasiƙu zuwa ga dukan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Zerzes. Saƙon fatan alheri da na tabbaci,
31
don a kafa waɗannan ranakun Furim a keɓaɓɓen lokacinsu, kamar yadda Mordekai mutumin Yahuda da Sarauniya Esta suka dokace su. Yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu, game da lokutansu na azumi da makoki.
32
Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan umarnai game da Furim, aka kuma rubuta ta cikin tarihi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options