Skip to content
Esta 9:17-22

Esta 9:17-22

17
Wannan ya faru a ran goma sha uku na watan Adar. A rana ta goma sha huɗu kuwa suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da kuma ta farin ciki.
18
Amma Yahudawan da suke a Shusha suka taru a rana ta goma sha uku da ta sha huɗu, sa’an nan a rana ta goma sha biyar suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da ta farin ciki.
19
Shi ya sa Yahudawan ƙauyuka, waɗanda suke zama a karkara, suke kiyaye rana ta goma sha huɗu ta watan Adar a matsayin ranar farin ciki da ta biki, ranar ba da kyautai ga juna.
20
Sai Mordekai ya rubuta waɗannan abubuwa, ya kuma aika wasiƙu ga dukan Yahudawa ko’ina a lardunan Sarki Zerzes, na kusa da na nesa.
21
Ya sa su yi bikin kowace shekara a ranaku goma sha huɗu da goma sha biyar na watan Adar
22
a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 90 chars

Options