Esta 7:4-6
4
Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.”
5
Sarki Zerzes ya tambayi Sarauniya Esta ya ce, “Wane ne shi? Ina mutumin da ya yi ƙarfin halin yin wannan karambani?”
6
Esta ta ce, “Maƙiyi da abokin gāban, shi ne wannan mugun Haman.” Sai Haman ya tsorota a gaban sarki da sarauniya.
Settings