Esta 7:7-10
7
Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa.
8
Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sarki ya tā da murya da ƙarfi ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya yayinda take tare da ni a cikin gida?” Sarki bai ma rufe baki ba, sai bayin sarki suka rufe fuskar Haman.
9
Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.” Sai sarki ya ce, “Ku rataye shi a kansa!”
10
Saboda haka suka rataye Haman a kan wurin rataye mai laifin da shi Haman ya shirya saboda Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce.
Settings