Skip to content
Esta 5:1-6

Esta 5:1-6

1
A rana ta uku, Esta ta sanya rigunanta na sarauta, ta tafi ta tsaya a harabar fada, a gaban zaure sarki. Sarki yana zaune a kan gadon sarautarsa a zauren, yana fuskantar ƙofar shiga.
2
Sa’ad da ya ga Sarauniya Esta tsaye a harabar, sai ya ji daɗin ganinta, ya miƙa mata sandan sarauta na zinariya da take hannunsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan.
3
Sai sarki ya ce mata, “Me kike so, Sarauniya Esta? Mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”
4
Esta ta ce, “In ya gamshi sarki, bari sarki, tare da Haman su zo wurin liyafar da na shirya wa sarki yau.”
5
Sai sarki ya ce, “Maza a kawo Haman don mu yi abin da Esta ta roƙa.” Saboda haka, sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya.
6
Yayinda suke shan ruwan inabi, sarki ya sāke ce wa Esta, “Yanzu, mece ce bukatarki? Za a biya miki shi. Kuma mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options