Esta 3:7-11
7
A shekara ta goma sha biyu ta Sarki Zerzes, a wata na farko, watan Nisan, sai suka jefa fur (wato, ƙuri’a) a gaban Haman don a zaɓi rana da watan da zai dace da ƙulle-ƙullen. Sai ƙuri’a ta fāɗa a kan wata na goma sha biyu, wato, watan Adar.
8
Sai Haman ya ce wa Sarki Zerzes, “Akwai waɗansu mutanen da suke a warwatse, sun kuma bazu a cikin mutane cikin dukan lardunan masarautarka, waɗanda al’adunsu sun yi dabam da na dukan sauran mutane. Mutanen nan ba sa biyayya da dokokin sarki; ba zai yi wa sarki kyau a jure su ba.
9
In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.”
10
Saboda haka sarki ya zare zoben hatimi daga yatsarsa, ya ba wa Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban Yahudawa.
11
Sarki ya ce wa Haman, “Ka riƙe kuɗin, ka kuma yi da mutanen yadda ka ga dama.”
Settings