Skip to content
Esta 3:12-15

Esta 3:12-15

12
Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.
13
Aka aika ’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu.
14
Za a ba da kofin rubutun a matsayin doka a kowane lardi, a kuma sanar da mutanen kowace al’umma, domin su zauna da shiri don wannan rana.
15
Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan-kada-tă-kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a mazaunin masarauta da yake a Shusha. Sai Sarki da Haman suka zauna don su sha, amma birnin Shusha ya ruɗe.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options