Skip to content
Afisawa 2:1-10

Ceto ta wurin alheri

Afisawa 2:1-10
1
Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku.
2
Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah.
3
Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah.
4
Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai,
5
ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.
6
Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.
7
Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu.
8
Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah.
9
Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.
10
Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options