Mai Hadishi 7:15-29
15
A cikin rayuwan nan ta rashin amfani nawa, na lura da waɗannan abubuwa biyu, mai adalci yana hallakawa cikin adalcinsa, mai mugunta kuma yana tsawon rai cikin muguntarsa.
16
Kada ka cika yin adalci, fiye da kima, kada kuma ka cika yin hikima, don me za ka hallaka kanka!
17
Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, don me za ka mutu kafin lokacinka?
18
Yana da kyau ka kama ɗaya ba tare da ka saki wancan ba. Mai tsoron Allah zai guji wuce gona da iri.
19
Hikima takan sa mutum guda mai hikima yă yi ƙarfi fiye da masu mulki goma a cikin birni.
20
Babu mai adalci a duniya wanda yake yin abin da yake daidai da bai taɓa yin zunubi ba.
21
Kada ka mai da hankali ga dukan abin da mutane suke faɗi, in ba haka ba wata rana za ka ji bayinka suna zaginka.
22
Gama kai kanka ka sani cewa sau da yawa ka zagi waɗansu.
23
Dukan waɗannan na gwada su ta wurin hikima na kuma ce, “Na ƙudurta in zama mai hikima,” amma abin ya fi ƙarfina.
24
Ko da me hikima take, Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa, wa zai iya gane shi?
25
Saboda haka na mai da hankalina ga fahimi, don in bincika in nemi hikima da yadda aka tsara abubuwa, in kuma fahimci wawancin mugunta da haukar wauta.
26
Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci mace wadda take tarko ne, wadda zuciyarta tarko ne wadda kuma hannuwanta sarƙa ne. Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata, amma za tă kama mai zunubi.
27
Malami ya ce, “Duba, abin da na gane ke nan. “Na tara abu guda da wani, don in gane tsarin abubuwa,
28
yayinda nake cikin nema amma ban samu ba, sai na sami adali guda cikin dubu, amma ba mace mai adalci guda a cikinsu duka.
29
Wannan ne kaɗai abin da na gane. Allah ya yi mutum tsab amma sai muka rikitar da kanmu.”
Settings