Mai Hadishi 7:1-14
1
Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.
2
Gara a tafi gidan makoki da a je gidan biki, gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum; ya kamata masu rai su lura da haka.
3
Baƙin ciki ya fi dariya, gama baƙin ciki yakan kawo gyara.
4
Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki, amma zuciya wawaye tana a gidan shagali.
5
Gara ka saurari tsawatawar mai hikima da ka saurari waƙar wawaye.
6
Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya, haka dariyar wawaye take. Wannan ma ba shi da amfani.
7
Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa, cin hanci kuma yakan lalace hali.
8
Ƙarshen abu ya fi farkonsa, haƙuri kuma ya fi girman kai.
9
Kada ranka yă yi saurin tashi, gama fushi yana zama a cinyar wawaye.
10
Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi waɗannan?” Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi.
11
Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana.
12
Hikima mafaka ce takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi. Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita ita ce amfanin ilimi.
13
Ku lura da abin da Allah ya yi. Wa zai iya miƙe abin da ya tanƙware?
14
Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki, amma sa’ad da suka lalace, ka tuna, Allah ne ya yi wancan shi ne kuma ya yi wannan. Saboda haka, mutum ba zai san wani abu game da nan gabansa ba.
Settings