Skip to content
Mai Hadishi 6:10-12

Mai Hadishi 6:10-12

10
Duk abin da ya kasance, to, yana da suna, kuma duk abin da mutum yake, an riga an sani. Ba mutumin da zai iya ƙarawa da wanda ya fi shi ƙarfi.
11
Yadda yawan magana take haka ƙarancin amfaninta, yaya wannan zai amfane wani?
12
Gama wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a ’yan kwanakinsa marasa amfani da sukan wuce kamar inuwa? Wa kuma zai iya faɗa masa abin da zai faru a duniya bayan ya rasu?
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options