Skip to content
Mai Hadishi 6:1-7

Mai Hadishi 6:1-7

1
Na ga wani mugun abu a duniya, ya kuma nawaita wa mutane ƙwarai.
2
Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai.
3
Mutum zai iya kasance da ’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa.
4
Haihuwa ba tă amfane wanda aka haifa gawa ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi.
5
Ko da yake bai ga hasken rana ba, bai kuma san kome ba, duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa ransa ba,
6
ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba?
7
Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa, duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options