Mai Hadishi 5:13-17
13
Na ga wani mugun abu a duniya, arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi,
14
ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara, har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa, babu abin da ya bar masa.
15
Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa, kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma. Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa da zai riƙe a hannunsa.
16
Wannan ma mugun abu ne, Yadda mutum ya zo, haka zai koma, to, wace riba ce ya ci, da yake ya yi wahalar iska ce kawai?
17
Duk rayuwarsa ya ci abinci a cikin duhu, da ɓacin rai mai tsanani, da azaba, da fushi.
Settings