Mai Hadishi 5:10-17
10
Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani.
11
Kamar yadda kaya suke haɓaka, haka ma masu amfani da su. Kuma wane amfani ne suke ga mai shi in ba ciyar da idanunsa a kansu ba?
12
Barcin ma’aikaci daɗi gare shi, ko yă ci kaɗan ko da yawa, amma yalwar mai arziki ba ta barinsa yă iya yin barci.
13
Na ga wani mugun abu a duniya, arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi,
14
ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara, har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa, babu abin da ya bar masa.
15
Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa, kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma. Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa da zai riƙe a hannunsa.
16
Wannan ma mugun abu ne, Yadda mutum ya zo, haka zai koma, to, wace riba ce ya ci, da yake ya yi wahalar iska ce kawai?
17
Duk rayuwarsa ya ci abinci a cikin duhu, da ɓacin rai mai tsanani, da azaba, da fushi.
Settings