Mai Hadishi 4:1
Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Na sāke dubawa sai na ga zaluncin da ake yi a duniya. Na ga hawayen waɗanda ake zalunta kuma ba su da mai taimako; masu iko suna goyon bayan masu zalunci, ga shi ba su da mai taimako.
2
Sai na furta cewa matattu, waɗanda suka riga suka mutu, sun fi waɗanda suke a raye farin ciki, waɗanda har yanzu suke da rai.
3
Amma wanda ya fi su duka shi ne wanda bai riga ya kasance ba, wanda bai ga muguntar da ake yi a duniya ba.
4
Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
Settings