Mai Hadishi 3:1-10
1
Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2
Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3
Lokacin kisa da lokacin warkarwa, lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4
Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa.
5
Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su, lokacin runguma da lokacin dainawa.
6
Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya, lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7
Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana.
8
Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama.
9
Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa?
10
Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane.
Settings