Maimaitawar Shari’a 31:3
Ana nuna aya 3 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Sai Musa ya fita ya kuma faɗa waɗannan kalmomi ga dukan Isra’ila cewa,
2
“Yanzu shekaruna ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji ya ce mini, ‘Ba za ka haye Urdun ba.’
3
Ubangiji Allahnku kansa zai haye a gabanku. Zai hallaka waɗannan al’ummai da suke gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu. Yoshuwa shi ma zai haye a gabanku, yadda Ubangiji ya faɗa.
4
Ubangiji zai yi da su, yadda ya yi da Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, waɗanda ya hallaka tare da ƙasarsu.
5
Ubangiji zai bashe su gare ku, dole kuma ku yi musu dukan abin da na umarce ku.
6
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
Settings