Maimaitawar Shari’a 23:9-14
9
Sa’ad da kuka yi sansani don ku yi yaƙi da abokan gābanku, ku kiyaye kanku daga duk wani abu marar tsabta.
10
In ɗaya daga cikin mazanku ya ƙazantu saboda zubar da maniyyi, sai yă fita daga sansani yă zauna waje da sansani.
11
Amma yayinda yamma ke gabatowa sai yă wanke kansa, da fāɗuwar rana kuwa sai yă koma cikin sansani.
12
Ku keɓe wuri waje da sansani inda za ku iya zuwa don yin bayan gari.
13
Sai ku ɗauki wani abin tona ƙasa, sa’ad da kuka yi bayan gari, sai ku tona rami, ku rufe bayan garinku.
14
Gama Ubangiji Allahnku yana zagawa a cikin sansaninku don yă tsare ku, yă kuma bashe abokan gābanku gare ku. Dole sansaninku yă kasance da tsarki, saboda kada yă ga wani abu marar kyau a cikinku, har yă juya daga gare ku.
Settings