Skip to content
Maimaitawar Shari’a 16:9-15

Maimaitawar Shari’a 16:9-15

9
Ku ƙirga makoni bakwai, wato, ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye.
10
Sa’an nan ku yi shagalin Bikin Makoni ga Ubangiji Allahnku, ta wurin ba da hadaya ta yardar rai daidai da albarkun da Ubangiji Allahnku ya yi muku.
11
Ku kuma yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawan cikin biranenku, har ma da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikinku.
12
Ku tuna fa, dā ku bayi ne a Masar, sai ku lura, ku bi waɗannan ƙa’idodi.
13
Ku yi shagalin Bikin Tabanakul har kwana bakwai, bayan kuka gama tattara amfanin gona daga masussukarku da kuma daga wuraren matsin inabinku.
14
Ku yi farin ciki a Bikinku, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawa, da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikin biranenku.
15
Kwana bakwai za ku yi shagalin Bikin ga Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa. Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan girbinku da kuma cikin dukan aikin hannuwanku, farin cikinku kuwa zai cika.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options