Skip to content
Maimaitawar Shari’a 16:1-8

Maimaitawar Shari’a 16:1-8

1
Ku kiyaye watan Abib, ku kuma yi shagalin Bikin Ƙetarewar Ubangiji Allahnku, domin a watan Abib ne ya fitar da ku daga Masar da dad dare.
2
Ku miƙa ’yar dabba daga cikin garkenku na tumaki, ko na shanu a matsayin Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa.
3
Kada ku ci shi da burodin da aka yi da yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, burodi ne na wahala, gama kun bar Masar da gaggawa, saboda haka dukan kwanakin rayuwarku za ku tuna da lokacin da kuka fita daga Masar.
4
Kada a iske yisti a cikin mallakarku a dukan ƙasarku har kwana bakwai. Kada ku bar wani nama na hadayar da kuka yi a yammancin ranar farko, yă kwana har safe.
5
Kada ku miƙa hadayar Bikin Ƙetarewa a wani garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku,
6
sai dai a wurin da ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa. A can za ku miƙa hadayar Bikin Ƙetarewa da yamma, sa’ad da rana tana fāɗuwa, a ranar tunawa da fitowarku daga Masar.
7
Ku gasa shi, ku kuma ci a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sa’an nan da safe, ku dawo cikin tentunanku.
8
Kwana shida za ku ci burodi marar yisti, a rana ta bakwai kuma sai ku yi taro ga Ubangiji Allahnku, a cikin wannan rana ba za ku yi kowane irin aiki ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options