Maimaitawar Shari’a 14:3-20
3
Kada ku ci wani haramtaccen abu.
4
Waɗannan su ne dabbobin da za ku iya ci, saniya, tunkiya, akuya,
5
mariri, barewa, mariya, makwarna, mazo, gada da kuma tunkiyar dutse.
6
Za ku iya cin duk dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take sāke tona abin da suka riga suka haɗiye.
7
Amma, cikin waɗanda suke sāke tona abin da suka riga suka haɗiye ɗin, ko suke da rababben kofato, ba za ku ci raƙumi, zomo ko rema ba. Ko da yake suna sāke tona abin da suka riga suka haɗiye, suna kuma da rababben kofato, su ɗin marar tsarki ne gare ku.
8
Alade ma marar tsarki ne; ko da yake yana da rababben kofato, shi ba ya sāke tona abin da ya riga ya haɗiye. Ba za ku ci namansu ko ku taɓa gawarsu ba.
9
Cikin dukan halittun da suke cikin ruwa, za ku iya cin duk wani da yake da ƙege da ɓamɓaroki.
10
Amma duk wani abin da ba shi da ƙege da ɓamɓaroki, ba za ku ci ba; gama marar tsarki ne gare ku.
11
Za ku iya cin kowane tsuntsu mai tsabta.
12
Amma waɗannan ba za ku ci ba, gaggafa, ungulu, ungulun kwakwa,
13
duki, buga zaɓi, kowace irin shirwa,
14
kowane irin hankaka,
15
jimina, ƙururu, bubuƙuwa, kowane irin shaho,
16
da mujiya, da babbar mujiya, ɗuskwi,
17
kwasakwasa, ungulu, da babba da jaka,
18
zalɓe, kowane irin jinjimi, katutu, da kuma jamage.
19
Dukan ’yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe, haram ne a gare ku, kada ku ci su.
20
Amma duk wata halitta mai fikafikai mai tsabta ce, za ku iya ci.
Settings