Maimaitawar Shari’a 14:22-27
22
Ku tabbata kun keɓe kashi ɗaya bisa goma na amfanin gonakinku kowace shekara.
23
Ku ci zakkar hatsinku, da na sabon ruwan inabinku, da na manku, da kuma na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, don ku koyi girmama Ubangiji Allahnku kullum.
24
Amma in wurin nan yana da nisa sosai, Ubangiji Allahnku kuma ya albarkace ku, ba za ku kuwa iya riƙe zakkarku ba (Saboda wurin da Ubangiji ya zaɓa yă sa Sunansa ya yi nisa sosai),
25
to, sai ku sayar da zakkar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa.
26
Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki.
27
Kada dai ku manta da Lawiyawan da suke zama a biranenku, gama ba su da rabo, ko gādo na kansu.
Settings