Skip to content
Maimaitawar Shari’a 12:5-18

Maimaitawar Shari’a 12:5-18

5
Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin dukan kabilanku, inda zai sa Sunansa, yă mai wurin mazauninsa. A wannan wuri ne za ku tafi;
6
a can ne kuma za ku kawo hadayun ƙonawa da sadakoki, zakkarku da kyautai na musamman, da abin da kuka yi alkawari za ku bayar, da hadayunku na yardar rai, da kuma ’ya’yan farin garkunanku na shanu da na tumaki.
7
A can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku da iyalanku za su ci, su kuma yi farin ciki a kome da kuka sa hannunku a kai, domin Ubangiji Allahnku zai albarkace ku.
8
Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama.
9
Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna.
10
Amma sa’ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, zai kuwa ba ku hutu daga dukan abokan gābanku da suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya,
11
sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa.
12
A can kuma za ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, waɗanda ba a ba su rabo ba, ba su kuma da gādo na kansu.
13
Ku kula fa kada ku miƙa hadayun ƙonawa a wani wurin da kuka ga dama.
14
Ku miƙa su kawai a wurin da Ubangiji zai zaɓa a cikin ɗaya daga kabilanku, a can za ku yi kowane abin da na umarce ku.
15
Amma kwa iya yanka nama ku ci a garuruwanku, a duk lokacin da ranku yake so, kamar yadda ake yi da gada ko barewa, bisa ga albarkar da Ubangiji Allahnku yake sa muku. Marar tsarki da mai tsarki, duka za ku iya ci.
16
Amma kada ku ci jini, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
17
Kada ku ci zakkar hatsi, da na sabon inabi, da kuma na mai a biranenku, ko kuwa na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki, ko kuwa duk wani abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ko hadayunku na yardar rai, ko kyautai na musamman.
18
A maimakon haka, sai ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, ku kuwa yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a kowane abin da kuka sa hannunku.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options