Skip to content
Maimaitawar Shari’a 12:15-28

Maimaitawar Shari’a 12:15-28

15
Amma kwa iya yanka nama ku ci a garuruwanku, a duk lokacin da ranku yake so, kamar yadda ake yi da gada ko barewa, bisa ga albarkar da Ubangiji Allahnku yake sa muku. Marar tsarki da mai tsarki, duka za ku iya ci.
16
Amma kada ku ci jini, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
17
Kada ku ci zakkar hatsi, da na sabon inabi, da kuma na mai a biranenku, ko kuwa na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki, ko kuwa duk wani abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ko hadayunku na yardar rai, ko kyautai na musamman.
18
A maimakon haka, sai ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, ku kuwa yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a kowane abin da kuka sa hannunku.
19
Ku yi hankali, kada ku manta da Lawiyawa, muddin kuna zaune a ƙasarku.
20
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya fadada iyakarku kamar yadda ya yi muku alkawari, kuka kuma ji marmarin nama, kuka kuma ce, “Muna so mu ci nama,” to, za ku iya cin yadda kuke so.
21
In wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don yă sa Sunansa yana da nisa sosai daga inda kuke, za ku iya yankan dabbobi daga garkunanku na shanu da na tumakin da Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku, a cikin biranenku kuma za ku iya ci, yadda kuke so.
22
Ku ci su yadda akan ci barewa ko mariri. Marar tsarki da mai tsarki, za ku iya ci.
23
Amma ku tabbata ba ku ci jinin ba, domin jini ne rai, ba kuwa za ku ci rai cikin naman ba.
24
Ba za ku ci jini ba, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
25
Kada ku ci shi, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
26
Amma ku ɗauki abubuwa masu tsarki, da kuma duk abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ku tafi inda Ubangiji ya zaɓa.
27
Ku miƙa hadayunku na ƙonawa a bagaden Ubangiji Allahnku, da naman da kuma jinin. Dole a zub da jinin hadayunku a gindin bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku iya cin naman.
28
Ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan waɗannan umarnan da nake ba ku, da kuma ’ya’yanku, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai da kuma yake mai kyau a gaban Ubangiji Allahnku.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options