Daniyel 7:15-27
15
“Ni, Daniyel, ruhuna ya damu ƙwarai, kuma wahayin da ya ratsa tunanina ya dame ni.
16
Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a can, na tambaye shi gaskiya ma’anar waɗannan al’amura. “Don haka sai ya faɗa mini, ya kuma ba ni fassarar waɗannan al’amura.
17
‘Waɗannan manyan dabbobi huɗu, Masarautai ne huɗu waɗanda za su taso a duniya.
18
Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’
19
“Sa’an nan kuma sai na so in san ma’anar wannan dabba ta huɗu, wadda ta yi dabam da sauran dabbobin da suke da matuƙar bantsoro, da take da haƙoran ƙarfe da kuma farcen tagulla, dabbar ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta.
20
Na kuma so in gane game da ƙahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ƙahon nan da ya fito, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa, ƙahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma.
21
Ina cikin dubawa, sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka yana kuma cin nasara a kansu,
22
sai da Wannan wanda yake tun fil azal ya zo ya furta hukunci, aka kuma ba tsarkaka na Mafi Ɗaukaka gaskiya, lokaci kuwa ya cika sai suka karɓi mulki.
23
“Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta.
24
Ƙahonin nan goma, sarakuna ne goma waɗanda za su taso daga wannan mulki. Bayansu kuma, wani sarki zai taso, wanda ya sha dabam da waɗanda suka riga shi. Zai rinjayi sarakunan nan uku.
25
Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci.
26
“ ‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada.
27
Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’
Settings