Daniyel 1:1-4
1
A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya.
2
Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon cikin ma’ajin gidan allahnsa.
3
Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane.
4
Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu.
Settings