Skip to content
Kolossiyawa 1:15-23

Kolossiyawa 1:15-23

15
Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta.
16
Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne.
17
Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.
18
Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici.
19
Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi,
20
ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.
21
A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku.
22
Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.
23
Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options