Amos 6:8-14
8
Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta, “Ina ƙyamar girman kan Yaƙub, ba na kuma son kagarunsa; zan ba da birnin da duk abin da yake cikinta.”
9
Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu.
10
In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”
11
Gama Ubangiji ya ba da umarni, zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.
12
Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu? Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma? Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi amfanin adalci kuma ya zama ɗaci,
13
ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar da yaƙi kuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim ba?”
14
Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce, “Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila, wadda za tă matsa muku tun daga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba.”
Settings