Skip to content
Amos 5:10-15

Amos 5:10-15

10
Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a kuna ƙin mai faɗar gaskiya.
11
Kuna matsa wa matalauta kuna sa su dole su ba ku hatsi. Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, ba za ku zauna a cikinsu ba; ko da yake kun nome gonaki masu kyau, ba za ku sha ruwan inabinsu ba.
12
Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.
13
Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, gama lokutan mugaye ne.
14
Ku yi nagarta, ba mugunta ba; don ku rayu sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku, kamar yadda kuka ce zai yi.
15
Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin raguwar Yusuf.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options