Amos 2:9-12
9
“Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama, da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.
10
Na fitar da ku daga ƙasar Masar, na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada don in ba ku ƙasar Amoriyawa.
11
“Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” In ji Ubangiji.
12
“Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.
Settings