Skip to content
Ayyukan Manzanni 9:1-22

Ayyukan Manzanni 9:1-22

1
Ana cikin haka, Shawulu ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist
2
ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majami’un Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yă kama su a matsayin ’yan kurkuku yă kai Urushalima.
3
Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.
4
Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”
5
Shawulu ya yi tambaya ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.
6
Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”
7
Mutanen da suke tafiya tare da Shawulu suka rasa bakin magana; sun ji muryar amma ba su ga kowa ba.
8
Shawulu ya tashi daga ƙasa, amma sa’ad da ya buɗe idanunsa bai iya ganin wani abu ba. Saboda haka aka kama hannunsa aka yi masa jagora zuwa cikin Damaskus.
9
Kwana uku yana a makance, bai ci ba bai kuma sha kome ba.
10
A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”
11
Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a.
12
Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don yă sāke samun ganin gari.”
13
Ananiyas ya amsa ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.
14
Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don yă kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.”
15
Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don yă kai sunana a gaban Al’ummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Isra’ila.
16
Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”
17
Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”
18
Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawulu, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma,
19
bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi. Shawulu ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus.
20
Nan take ya fara wa’azi cikin majami’u cewa Yesu Ɗan Allah ne.
21
Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki suka ce, “Ba shi ne mutumin da ya tā-da-na-zaune-tsaye a kan masu kira bisa ga wannan sunan a Urushalima ba? Ba ya zo nan ne don yă kai su a matsayin ’yan kurkuku ga manyan firistoci ba?”
22
Duk da haka Shawulu ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options