Ayyukan Manzanni 8:38-39
38
Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma.
39
Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.