Ayyukan Manzanni 26:9-18
9
“Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare.
10
Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su.
11
Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.
12
“A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci.
13
Da tsakar rana, ya sarki, sa’ad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata.
14
Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’
15
“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.
16
Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka.
17
Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin
18
ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’
Settings