Skip to content
Ayyukan Manzanni 26:24-29

Festus da Agaribas Sun Amsa

Ayyukan Manzanni 26:24-29

Festus da Agaribas Sun Amsa

24
A nan ne fa Festus ya tsai da kāriyar Bulus. Ya yi ihu ya ce, “Bulus! Kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”
25
Bulus ya amsa ya ce, “Ba na hauka, ya mafifici Festus. Abin da nake faɗi gaskiya ne da kuma mai kyau.
26
Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba.
27
Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.”
28
Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?”
29
Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.”

Duba kuma

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • 1 Korintiyawa 1:23

    amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai,
    daga aya ta 24
  • 1 Korintiyawa 2:13

    Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya.
    daga aya ta 24
  • 1 Korintiyawa 2:14

    Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.
    daga aya ta 24
  • 1 Korintiyawa 4:10

    Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu!
    daga aya ta 24
  • 2 Korintiyawa 5:13

    In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne.
    daga aya ta 24
  • Markus 3:21

    Da ’yan’uwansa suka sami wannan labari, sai suka tafi don su dawo da shi, suna cewa, “Ai, ya haukace.”
    daga aya ta 24
  • Ayyukan Manzanni 11:26

    sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista.
    daga aya ta 28
  • 2 Sarakuna 9:11

    Da Yehu ya koma wurin sauran hafsoshin sai ɗaya daga cikinsu ya tambaye shi, “Lafiya? Me ya kawo wannan mahaukaci a wurinka?” Sai Yehu ya ce, “Ka san mahaukacin nan da irin maganganunsa.”
    daga aya ta 24
  • Ayyukan Manzanni 26:11

    Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.
    daga aya ta 24
  • Irmiya 29:26

    ‘Ubangiji ya naɗa ka firist a wurin Yehohiyada don ka lura da gidan Ubangiji; ya kamata ka sa kowane mahaukaci wanda yake yi kamar annabi cikin turu da kuma a kangi.
    daga aya ta 24
  • Ayyukan Manzanni 23:26

    Kalaudiyus Lisiyas. Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis. Gaisuwa.
    daga aya ta 25
  • Ayyukan Manzanni 26:2

    Ya ce, “Sarki Agiriffa, na yi sa’a da na tsaya a gabanka yau yayinda nake kāriyata game da dukan zargin Yahudawa,
    daga aya ta 26

Inda wannan ya faru

All Acts Sites (Eastern Mediterranean)
All Acts Sites (Eastern Mediterranean) View full PDF
Overview of Paul's Journeys
Overview of Paul's Journeys View full PDF

Map © Biblica Open Bible Maps · CC BY-SA 4.0

Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options