- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Biyayya ga Kiran Sama
Ayyukan Manzanni 26:19-23
Biyayya ga Kiran Sama
19
“Saboda haka fa, Sarki Agiriffa, ban yi rashin biyayya ga wahayin nan daga sama ba.
20
Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, sa’an nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Al’ummai su ma, na yi wa’azi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu.
21
Shi ya sa Yahudawa suka kama ni a filin haikali suka kuma yi ƙoƙarin kashe ni.
22
Amma na sami taimakon Allah har yă zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru,
23
cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai.”
Nazarin nassin nan
Sharhi a kan nassin, ba aya ɗaya ba
- Su wane
- Ina
- Yaushe
- About
Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka
Ayyukan Manzanni 3:19
Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,daga aya ta 20Mattiyu 3:8
Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.daga aya ta 20Ishaya 50:5
Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana, kuma ban yi tayarwa ba; ban ja da baya ba.daga aya ta 192 Timoti 2:25
Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya,daga aya ta 202 Timoti 2:26
su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.daga aya ta 20Ayyukan Manzanni 2:38
Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.daga aya ta 20Ishaya 53:1
Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?daga aya ta 23Ishaya 53:12
Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.daga aya ta 23Luka 24:26
Ai, dole Kiristi yă sha waɗannan wahalolin, kafin yă shiga ɗaukakarsa.daga aya ta 23Ezekiyel 2:7
Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su ’yan tawaye ne.daga aya ta 19Ezekiyel 2:8
Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan ’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.”daga aya ta 19Galatiyawa 1:16
yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba.daga aya ta 19


Bayanin Nazari
Settings