Tsallake zuwa abun ciki
Ayyukan Manzanni 26:1-3

Bulus ya Yi Magana da Sarki Agaribas

Ayyukan Manzanni 26:1-3
1
Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “An ba ka izini ka yi magana.” Saboda haka Bulus ya yi alama da hannunsa ya fara kāriyarsa.
2
Ya ce, “Sarki Agiriffa, na yi sa’a da na tsaya a gabanka yau yayinda nake kāriyata game da dukan zargin Yahudawa,
3
musamman ma domin ka saba sosai da dukan al’adun Yahudawa da kuma maganganunsu. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options