Skip to content
Ayyukan Manzanni 2:22

Ayyukan Manzanni 2:22

Ana nuna aya 22 tare da mahallin da ke kewaye.
19
Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.
20
Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.
21
Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’
22
“Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.
23
An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.
24
Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
25
Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options