Ayyukan Manzanni 2:22-36
22
“Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.
23
An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.
24
Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
25
Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.
26
Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna, jikina kuma zai kasance da bege,
27
gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
28
Ka sanar da ni hanyoyin rai, za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’
29
“’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau.
30
Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.
31
Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba.
32
Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.
33
An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.
34
Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,
35
sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’
36
“Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”
Settings