Ayyukan Manzanni 19:23-34
23
Kusan wannan lokaci sai aka yi wani babban hargitsi game da wannan Hanyar.
24
Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba.
25
Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a.
26
Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan.
27
Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.”
28
Da suka ji haka, sai suka yi fushi ƙwarai suka fara ihu suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
29
Jim kaɗan sai hayaniya ta tashi a dukan birnin. Sai mutane suka cafke Gayus da Aristarkus, abokan tafiyar Bulus daga Makidoniya, suka ruga da zuwa fili da nufi ɗaya.
30
Bulus ya so ya bayyana a gaban taron, amma almajirai ba su bar shi ba.
31
Har waɗansu shugabannin lardin ma, abokan Bulus, suka aika masa suna roƙonsa kada yă kuskura ya shiga filin nan.
32
Taron kuwa ya ruɗe. Waɗansu suna ihu suna ce abu kaza, waɗansu kuma wani abu dabam. Yawancin mutane kuma ba su ma san abin da ya sa suke a wurin ba.
33
Yahudawa suka tura Alekzanda gaba, sai waɗansu a taron suka riƙa yin masa ihu. Sai ya ɗaga hannu don a yi shiru don yă kāre kansa a gaban mutane.
34
Amma sa’ad da suka gane shi mutumin Yahuda ne, sai duk suka yi ihu gaba ɗaya na kusa sa’a biyu, suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
Settings